Tutorials

Numbobin Sirri Na Layikan Waya Wadanda Ba Kowane Yasansu Ba Amma Wasu Suna Bukatarsu.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Numbobin Sirri Na Layikan Waya Wadanda Ba Kowane Yasansu Ba Amma Wasu Suna Bukatarsu

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakuyi Amfani Da Wasu Numbobi Dazamu Baku Su Wadanda Da Yawan Mutane Basu San Wadannan Numbobi Ba.

Amma Kafin Mukai Ga Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wannan Numbobi Muna Fatan Zamu Karanta Wannan Bayani Tundaga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake.

To Da Farko Dai Wadannan Numbobi Ba Kowane Numbobi Bane Face Nimbers Wadanda Zaku Iya Duba Number Din Wayoyinku.

Dalilin Dayasa Mukace Zamu Kawo Muku Wannan Darasi Dai Shine Saboda Wasu Mutane Da Dama Haryanzu Suna Da Wayar Android Ko Keypad Amma Haryanzu Basu San Yadda Zasu Duba Number Din Wayarsu Ba.

Wasu Zakaga Idan Sukason Duba Number Din Wayarsu Sai Sun Dauko Manual Din Layin Wasu Kuma Sai Sun Shiga Cikin Ko Wurin Da Suke Saving Na Contact Dinsu.

To A Yau Zamu Kawo Muku Wata Hanya Mai Sauki Wadda Zatayi Matukar Taimaka Muku Wurin Duba Number Din Wayoyinku Kuma Ko Wane Irin Layi Kake Amfani Dashi.

Amma A Shawarce Yana Dakyau Kowa Yayi Kokari Ya Haddace Number Din Wayarsa Tinda Ba Wani Yawane Garesu Dukka Dukkansu Fa Basu Wuce Goma Sha Daya Ba.

Amma Sai Kaga Mutane Da Dama Basu Haddacesu Ba, Alhalin Saikaga Mutum Ya Haddace Wata Banzar Waka Ma Amma Phone Number Tasa ta Gagareshi Haddacewa.

To A Yanzu Zamu Ajiye Muku Numbobin Da Zakuyi Amfani Dasu Idan Kanaso Kasan Number Din Wayarka Ta Kowane Layi Kama Daga Mtn Etisalat Airtel Ko Glo.

MTN : Idan Kana Da Layin MTN Kanaso Kasan Number Din Wayarka To Kai Tsaye Zaka Shiga Inda Kake Saving Na Number Ko Kake Dialing Saika Danna : *663#.

Kana Danna Wannan Number Take Phone Number Dinka Zata Bayyana Saika Bawa Wanda Kake Son Bawa Ko Kayi Abinda Kakeson Yi Da Ita.

Sai Layi Na Biyu Wanda Shine Airtel, Idan Kanaso Kasan Numbar Wayarka Ta AIRTEL To Kai Tsaye Zaka Danna : *121*3*4#.

Kana Danna Wannan Numbobin Take Itama Number Din Wayarka Ta Airtel Zata Bayyana Akan Screen Din Wayarka Zaka Iya Yin Abinda Kake Bukata Da Ita.

Layi Na Uku Wanda Shima Zaka Iya Duba Number Din Wayarsa Shine Etisalat, Idan Kanaso Kasan Number Dinka Na Etisalat To Kai Tsaye Zaka Danna : *248#.

To Shima Wannan Kana Danna Wannan Number Din Zakaga Number Dinka Ta Etisalat Ta Bayyana Akan Screen Din Wayarka.

Layi Na Karshe Wanda Muke Amfani Dashi A Nigeria Shine Layin Glo Wanda Shi Wannan Layi Ba Kowane Da Kowa Yake Amfani Dashiba.

Amma Duk Da Haka Zamuyi Kokari Shima Mu Ajiye Muku Number Din Dazaku Danna Idan Kunaso Kusan Number Din Wayarku.

Abinda Zaka Danna Shine : *135*8#
Kana Danna Wadannan Numbobi Take Zakaga Number Din Wayarka Ta Bayyana Akan Fuskar Wayarka.

Mungode Mungode Mungode Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi namu Mai Albarka Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!